About

Game da mu

Al-Huda Online Academy

Wannan makaranta ta Al-Huda Online Academy hadafin ta shine samar da dama ga Al’ummar Musulmai masu magana da yaren hausa damar samun karatun Addinin Musulunci cikin sauƙi.

Ko mutum ma’aikaci ne bashi da lokaci da zai je makaranta domin neman ilimin Addini zai iya shiga wannan makaranta tamu domin ya amfana da darussan da muke gabatar wa a fannoni mabanbanta.

Karatuka da ake gabatarwa a wannan makaranta akwai wanda suke kyauta, akwai kuma wadda ake biyan kuɗi wanda bashi da yawa.

A yanzu zamu fara gabatar da wa’innan karatuka ne a manhajan Telegram. Zuwa nan gaba insha Allah zamu rinƙa ɗaura karatukan a wannan shafi namu.

Domin shiga wannan Makaranta sai ku danna nan.

Idan kuna da wasu shawarwari ko wasu tambayoyi zaku iya tuntuɓarmu ta Email, ko WhatsApp ko Telegram.

Muna godiya. Allah ya bamu ilimi mai amfani.

Join Us

Start your transformative educational journey with Al-Huda Online Academy today.

or call us at:
+2348039412473