Al-Huda Online Academy

Maraba da Zuwa

Tsangayar Neman ilimi cikin sauki

Assalamu Alaikum.
Muna muku maraba da ziyartar wannan makaranta tamu, wanda muka kirkire ta domin samar da dama ga Yan’uwa Musulmai su sami ingataccen ilimi na addini da na Larabci cikin sauki.

Meyasa zaka zabe mu?

Karatu cikin sauki

Muna gudanar da karatunmu cikin sauki ba tare da ka zauna a aji ba, da wayarka ko computan ka zaka yi karatu

Tsarin Karatu mai kyau

Muna da tsare tsare masu Kayatar wa wanda zamu tabbatar da cewa dalibi ya fahimci maddar da ake karantar dashi

Saukin Farashi

Karatukanmu akwai na kyauta, akwai wanda kuma biya akeyi, amma farashi mai sauki wanda ba zai gagari kowa ba.

Darussa

Ga Adadin darussan da muke karantarwa a wannan makaranta tamu, za’a kara wasu maddodin nan gaba.

Qur’ani da Tajwid

Wannan ya Kunshi koyon Karatun Al-Qur’ani da Tajwidi, da Hadda.

Arabiyya

Ya kunshi Koyon Hada baki, Nahwu, sarfu, balaga, Adab da sauransu.

Tauhidi

Darussanmu na Tauhidi ya Kunshi Darussa tun daga littafai na kasa kasa har zuwa manyan littafa na tauhidi

Fiqhu

Wannan Sashin ya kunshi darussan Fiqhu na Mazhababobin Musulunci

Karfafa Guiwa

Me kake Jira?

Ka sani dan’uwa, Ki sani Yar uwa, Allah ya halicce mu ne domin mu bauta masa, kuma baza mu bauta masa ba sai da ilimi. meye zai hana ka ka bada mintocin kadan a rana domin neman ilimin abinda aka halicce ka domin shi? kana da lokaci, zaka iya, ka tashi ka nemi ilimin addini, domin dashi ne zaka tsira.

Tsarin Karatun mu a takaice

Samu ilimin Addini a sawwake

Karatunmu muna gudanar dashi ne a Telegram, nan ba da jima wa ba zamu fara daura shi a wannan shafin namu insha Allah. kuma muna da tsari mabanbanta, kama daga aji na gama gari, da kuma ajujuwa na masu son karatu a kebance. ku tuntubemu domin karin bayani