Al-Huda Online Madrasa

Maraba da Zuwa

Tsangayar Neman ilimi cikin sauki

Assalamu Alaikum.
Maraba da ziyartar wannan makaranta tamu, wanda muka kirkire ta domin samar da dama ga Yan’uwa Musulmai Maza, Mata da yara su sami ingataccen ilimi na addini da na Larabci cikin sauki.
Domin shiga ajin kyauta danna nan.
Domin Shiga Cikakken Tsarin Makaranta da ake biya danna nan domin Tuntubar mu ta WhatsApp ko ku kiramu
+2348039412473

Meyasa zaku zabe mu?

Karatu cikin sauki

Muna gudanar da karatunmu cikin sauki ba tare da ka zauna a aji ba, da wayarka ko computan ka zaka yi karatu

Tsarin Karatu mai kyau

Muna da tsare tsare masu Kayatar wa wanda zamu tabbatar da cewa dalibi ya fahimci darasin da ake karantar dashi

Saukin Farashi

Karatukanmu akwai na kyauta, akwai wanda kuma biya akeyi, amma farashi mai sauki wanda babau Sauri.

Darussa

Ga Adadin darussan da muke karantarwa a wannan makaranta tamu, za’a kara wasu maddodin nan gaba.

Hada Baki

Ajin Koyon Hada Bakin Larabci, dalibi zai koyi yadda zai hada bakin larabci daga Farko

Arabiyya

Dalibi zai koyi magana da Larabci da Ka’idodin Larabci. Nahwu/Sarf

quran, book, holy, muslim, islamic, islam, religion, religious, quran, quran, quran, quran, quran

Qur’an

Dalibi Zai koyi karatun Al-Qur’ani da Tajweed, da Darussa da suka shafi Al-Qur’ani Mai girma.

Islamiyyat

Wannan Ajin ana yin darussa na Tauhid, Hadith, Fiqh, Sirah, Azkar, Addu’oi.

An open Quran on a wooden stand captures spiritual essence in a mosque.

Tafseer/Tarjama

a wannan aji za’a koya wa dalibi Tafseer da kuma Tarjama na Al-Qur’ani, da wasu hukunce hukunce da suka shafi Qur’ani.

Premium

Wannan Za’a bai wa dalibi zabi duk fannin da yake so ya koya za’a koya masa, za’a tsara masa lokacin karatu da kuma bashi kulawa ta musamman

Karfafa Guiwa

Me kuke Jira?

Ku sani Yan’uwa, Allah ya halicce mu ne domin mu bauta masa, kuma baza mu bauta masa ba sai da ilimi. meye zai hana ku bada mintoci kadan a rana domin neman ilimin abinda aka halicce ku domin shi? kuna da lokaci, zaku iya, ku tashi ku nemi ilimin addini, domin dashi ne zaku tsira duniya da lahira.

Tsarin Karatun mu a takaice

Samu ilimin Addini a sawwake

Karatukan mu muna gabatar dasu ne ta Manhajar WhatsApp. kowa zai iya shiga, kuma dalibi shi zai zabi lokacin karatun sa. Kuma Private ne ake karatun kowa ana tura masa nasa, ba Group bane.
komi rashin lokacin ku zaku iya karatu damu. tuntube mu domin neman karin bayani